Sa'o'i kadan bayan Kaddamar da jirgin sama na sojojin sama a jihar Kaduna mai suna "Tseigumi" shugaban ya zarce mahaifar shi inda zai jajjanta da sauran yan uwanshi game da rasuwar da suka samu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa mahaifar sa Daura inda zai yi ta'aziya game da rasuwar wasu yan uwan shi mata.
Shugaban ya samu tarba daga a tawagar gwamnan jihar a Katsina Aminu Bello Masari da na sarkin Katsina mai marataba Alhaji Abdulmumin Kabir yayin da jirgin sa ta sauka a fillin jirgi na umaru musa Yar'adua dake nan garin Katsina.
Shugaban zai taya sauran iyalen sa jaje tare da karbar baki masu zuwa mika ta'aziya da jajanta masu.
Shugaban ya rasa yan uwan shi mata Hajiya Aisha Alhaji Mamman wanda take matar babban dan uwan shi Alhaji Mamman tare da Hajiya Halima Dauda daya daga cikin yaran dan uwanshi.
Jim kadan bayan kaddamar da sabuwar jirgin sama mai leken asiri wanda rundunar sojojin sama suka kera a garin Kaduna mai suna "Tseigumi", shugaban ya zarce zuwa mahaifar shi.
Nan bada jimawa ba shugaban ya hau jirgi mai saukar angulu zuwa mahaifar sa Daura inda mai martaba sarkin Dauran Alhaji Umar Farouq da fadawan sa suka tarbe shi.
http://ift.tt/2syRvUi