Shugaban kasa ya jinjina ma tawagar super Eagles kan nasarar da ta samu na shiga wasan karshe na cin kofin CHAN
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjin ama tawagar super eagles bisa nasarar da ta samu kan kasar Sudan na shiga damar buga wasan karshe na gasar zama zakarun afrika (chan).
Shugaban ya bayyana farin cikin sa ga nasarar da yan wasan suka samu a shafin sa na twitter daren ranar laraba 31 ga wata.
"Ina taya tawagar super eagles na gida murna bisa nasara da ta samu kan Sudan a wasan daf da karshe na gasar CHAN a daren yau. Dubban yan kasa na taya ku murna kana muna sa ran kallon wasan karshe ranar lahadi da kyakyawar zato. Muna alfahari daku" shugaban ya rubuta.
Wasan daf da karshe da tawagar Nijeriya ta buga da kasar Sudan an tashi 1-0 wanda d-an wasan Gabriel Okechukwu ya sanya kwallo a ragar cikin minti 16 da fara wasa.
A wasan dai Nijeriya ta samu karancin dan wasa daya Ifeanyi Samuel wanda aka ba jan kati.
Nijeriya zata kara da kasar Morocco a wasan karshe bayan kasar arewacin afrika ta samu nasarar lashe makwabtar su Libya 3-1.
Tags:
News