A cewar shi yan ta'addar sunkai harin ne a daidai karfe 5:30 na yamma amma har ga lokac in da ya zanta da manema labarai ba samu adadin illar da harin ya haifar.
Kwamishnan yan sanda na jihar Yobe AbdulMaliki Sumonu ya tabbatar da harin ba zata da wasu yan ta'adda da akie zato yan boko haram ne suka kai garin Dapchi na karamar hukumar Bursari.
Kwamishnan ya tabbatar da faruwar hakjan yayin da ya zanta da manema labarai ranar litinin.
A cewar shi yan ta'addar sunkai harin ne a daidai karfe 5:30 na yamma amma har ga lokac in da ya zanta da manema labarai ba samu adadin illar da harin ya haifar.
Babban jami'in yan sanda ya sanar cewa an tura dakaru garin domin kawo sauki da tabbatar da tsaro a yankin.
Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa mazauna garin sun tsere zuwa daji domin kubita daga harin da yan ta'addar suka kai.
Yayin da manema suka zanta da shugaban karamar hukumar Bursari Alhaji Zanna Abatcha ya sanar cewa yan ta'addar sun tsere daga garin kuma an samu an tura dakarun jami'an tsaro garin domin tabbattar da tsaro.