Boko Haram: Sojoji sun ceto mata yan makaranta da yan ta'adda suka sace a jihar Yobe

Rundunar sojoji sun kashe yan ta'ada 11 a jihar Borno

Jami'an tsaron sun samu nasarar kubitar dasu a daidai garin Jalli-Muwarti dake iyakar jihar Yobe da Borno.

Rundunara sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto yan matan makaranta da yan ta'addar boko haram suka sace a garin Dapchi dake jihar Yobe.

Jami'an tsaron sun samu nasarar kubitar dasu a daidai garin Jalli-Muwarta dake iyakar jihar Yobe da Borno.

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da wannan babban nasarar da rundunar sojoji suka yi yammacin ranar laraba 21 ga wata

Kamar yadda majiya suka ruwaito yanzu haka an tafi da yan matan asibiti dake karamar hukumar Gaidam domin duba lafiyar su kana a zarce dasu Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Yan ta'adar sun saci yan matan ne a ranar litinin da ya gabata yayin da suka kai harin garin Dapchi.

Post a Comment

Previous Post Next Post