Adam Zango: Duk wanda ya yayi rigima a kaina ban yafe masa ba!

Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hanni wajen tayar da hayaniya.

Jarumi mai tauraro Adam A.Zango ya gargadi yan uwanshi kan mayar da martani mai tayar da rigima kan wadanda ke zagin sa a shafukar sada zumunta.

Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hanni wajen tayar da hayaniya.

"DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA....ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA" ya rubuta.

Idan ba'a manta ba a kwanan baya jarumin  da abokin aikin sa kuma kuma babban jigo na masana'antar kannywood Ali Nuhu sun samu sabani wanda ya tayar da iska tsakanin mabiyan su.

 

Duk da cewa jarumai sun sulhunta kansu bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki na masana'antar kannywood suka yi na neman kawo karshen rigimar dake tsakanin su wannan bai hana wasu daga cikin mabiyan sucigaba da yi ma juna kalaman batanci.

Bugu da kari game da wannan rigimar da jarumai suka yi, sannanne dan wasan barkwanci Ali Idris Muhammed wanda aka fi sani da Aliartwork  yayi fashin baki inda yake cewa sun kirkiro rigimar ne da ganga domin jawo hankalin jama'a.

 

Aliartwork dai ya bada misali da irin rigimar da jaruman suka yi a shekarun baya wanda ya haifar da tseigumi tsakanin al'umma masu bibiyan harkokin masana'antar kannywood.

Jarumin ya kara da cewa jaruman su biyu azzalumai ne tare da yin la'akarin da yanayin lokacin da yayi dasu tare da yi masu aikin sarrafa bidiiyo wanda bai tsinana abun kirki ba daga gare su duk da kokarin da yayi

Post a Comment

Previous Post Next Post