A jihar Zamfara: Yan bindiga sun kashe mutum 41 a garin karamar hukumar Zurmi

Anyi jana'izar matatun da yan bindigar suka kashe a jihar Zamfara

Wani shaidar gani da ido ya shaida cewa yan bindigar sun iso ne cikin babura ai dai dai hanyar kasuwar garin har suka bindige duk wani dake shigowa ko fita daga garin.

Akala mutum 41 suka rasu yayin da wasu yan bindiga suka bude wuta ga wasu yan kasuwa matafiya a garin Birani na karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara.

A bisa rahotanni, lamarin ya faru ne ranar alhamis 15 ga wata inda yan bindigar suka bude ma matafiyan wutan albarusai.

Wani shaidar gani da ido ya shaida cewa yan bindigar sun iso ne cikin babura ai dai dai hanyar kasuwar garin har suka bindige duk wani dake shigowa ko fita daga garin. Cikin kankanin lokaci har suka yi sanadiyar mutuwar mutane 41.

Bugu da kari shaidar Abdu Husseini ya sanar cewa wani dan acaba mai dauke da wata mata tare da yaran ta sun gamu da ajalin su sanadiyar harbin kuma daga bisani yan bindigar suka kone acabar nashi.

Wanan ba shi bane karo na farko da irin wannan harin ke faruwa a jihar Zamfara. A watan Nuwamba na bara a samu makamancin haka inda aka kai hari garin Mulki na karamarn hukumar Shinkafi har aka kashe mutane kusan ashirin da hudu tare da kona gidaje je da dama.

http://ift.tt/2EvpMVO

Post a Comment

Previous Post Next Post