Za'ayi taron kaddamar da wannan ofishin a babbar wurin taro dake jami'ar Ibadan a daidai karfe 11 na safe.
Jam'iyar APC reshin kudu maso gabashin kasar zata kaddamar da ofishin yakin neman zaben zarcewar shugaba Muhammadu Buhari ranar asabar 20 ga wata a garin Ibadan na jihar Oyo.
Ministan sadarwa Adebayo Shittu ya kirkiri wannan ofishin karkashin kungiya mai taken Buhari/Osinbajo Dynamic Support group.
Za'ayi taron kaddamar da wannan ofishin a babbar wurin taro dake jami'ar Ibadan a daidai karfe 11 na safe.
A cikin takardar sanarwa da ministan ya fitar, tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzo Kalu zaiyi jawabi a wajen taron.
Manyan baki da zasu halarci wajen taron sun hada da jigon jam'iyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani da tsohon ministan man fetur Don Etiebet da kuma gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi wanda shine jagoran taron.
Hakazalika ministan safuri Rotimi Amaechi da tsohon shugaban jam'iyar APC mai rikon kwarya Bisi Akande zasu halarci wajen taron.
A bangaren gwamnoni kuma akwai gwamnan jihar Kaduna da Osun da ta Ondo har da ta jihar Legas kamar yadda ya sanar a takardar da ya fitar.
Cikin jerin yan majalisa da zasu halarci bikin kaddamarwa akwai Sanata Abu Ibrahim mai wakiltar kudancin jihar Katsina tare da sanata Ali Ndume da sanata Ayo Akinyelure.