Ta dauki wannan mataki ba tare da yin la'akari da girman ta don cinma burinta bayan bata samun damar yin haka yayin da take kuruciya.
Dattijiya Priscilla Sitienei mai shekara 90 a duniya ta koma makarantar firamare domin koyan ilimi.
Mazauniyar yankin Uasin Gishu county na kasar Kenya ta koma aji ne domin ta koyi karatu domin samun damar karanta littafi mai tsarki na addinin kiristoci tare da yadda zata ringa tura sakonnin wayar salula.
Ta dauki wannan mataki ba tare da yin la'akari da girman ta don cinma burinta bayan bata samun damar yin haka yayin da take kuruciya.
Priscilla wanda aka fi kira da Gogo ta koma ajin makarantar firamare ba tare da jin kunya kasancewa a aji daya da yara wadanda ke tsaran tattaba kunnen ta.
Wata malama a makarantar da dattijiyar take ta jinjina mata tare da yaba mata bisa wannan kokarin da tayi tare da yin la'akari cewa wannan zai nuna ma sauran manyan gari cewa shekaru baza su hana mutum koyan ilimi.