Toh fa! Yadda barayi ke damfarar jama'a ta hanyar na'urar cire kudi ta ATM

Barawon da aka kama da yana damfarar jama'a ta hanyar ATM

A takardar sanarwa da jami'i dake hulda da jama'a ya fitar, hukumar yan sanda ta gano hanyar da barayi ke bi domin damfarar jama'a a shingen ATM

Hukumar yan sanda na jihar Bauchi ta gano hanyar da barayi ke damfarar jama'a ta hanyar na'urar ATM.

Jami'an sun gano hakan bayan da suka kama wani gawurtacen barawo mai aikata wannan laifi.

 

A takardar sanarwa da kakakin hukumar DSP Kamal Datti Abubakar ya fitar ranar laraba 24 ga wata, an gano cewa barayin suna lefewa ne a shingen ATM kana su fake da taimakon wadanda ke fuskantar wahala wajen amfani da na'urar wajen fitar da kudi.

Da kuddirin taimako sai su sauya katin da wata daban daidai da irin ta bankin mutum.

Jami'an sun gano hakan yayi da suke cafke wani gawurtacen barawo mai aikata wannan laifin.

Post a Comment

Previous Post Next Post