Yakubu ya ja kunnen su akan kada su kara aikata wani laifi kana ya umarce su da su mayar da doyar ga ainihin mai shi.
Wani kotu dake nan yankin Aso fada a jihar Nassarawa ta yanke ma wasu yan aikin kwadago biyu hukuncin zama a gian yari na tsawon wata shidda kan laifin satar doya kwaya 50.
Mai sharia Upside Yakubu ya baiwa masu laifin Habibu Kabiru mai shekaru 25 da Salisu Hamidu mai sjhekaru 22 damar yan beli da naira dubu biyar (N5,000).
Yakubu ya ja kunnen su akan kada su kara aikata wani laifi kana ya umarce su da su mayar da doyar ga ainihin mai shi.
A bayanin wanda ya gurfanar dasu gaban kotu Agabi Auta, wani mai suna Utume Clement mazaunin garin kudu nan mararraba ya kawo karar su a ofishin yan sanda dake nan mararraba ranar 22 ga watan disamba 2017.
Yace masu laifin tare da wani Musa Iliya wanda ya tsere sun tafi gonar wanda ya kai karar su har suka gurbe masa doya 50.
Karanta>> Kotu ta dakatar da korar da gwamna yayi
Mai hurfanarwa ya sanar cewa an kama su ne yayin da suke yunkurin sanya doyar cikin buhu.
Yace laifin su ya sabawa kundin tsarin mulki sashe 79, 347, 348 da 287 na babin zartar da hukunci.