Adesanya ya sanar cewa jirgin Mi-17 ya samu matsala yayin da sojojin ke hanyar gabatar da hari ranar litinin 8 ga wata 2018.
Jirgin sama na sojojin sama kirar Mi-17 wanda ake yakar yan Boko haram dashi yayi hatsari yayin da sojoji ke yunkuri kai ma yan ta'adda hari.
Shugaban fannin watsa labarai na NAF Air Commodore Olatokunbo Adesanya ya sanar da haka a wata takardada ya fitar.
Adesanya ya sanar cewa jirgin Mi-17 ya samu matsala yayin da sojojin ke hanyar gabatar da hari ranar litinin 8 ga wata 2018.
kakakin ya tabbatar cewa babu wanda ya rasu sakamakon hatsarin
"Babban hafsan sojojin sama na kasa Air marshal Sadique Abubakar ya bada umarni na gaggawa na kafa yan bincike domin gano silar hatsari kamar yadda ake yi a fadin duniya.
har yanzu kuma NAF tana kira ga jama'a da su cigaba a goyon bayan rundunar sojoji yayin da suke kokarin tabbatar da tsaro ga yan kasa da ma kasar baki daya" kamar yadda aka rubuta a takardar da kakakin ya fitar.
Wani janar yayi barazanar kashe shugaban kasa Muhammadu Buhari
Makamancin haka ya faru a 2017
A cikin watan Yuli na bara wani jirgin sama na sojoji ya samu hatsari inda har ta fada cikin ruwa a wani bangaren arewa maso gabas na kasar.
Hakazalika cikin watan Agusta na 2017, wani jirgin rundunar NAF ya samu hatsari a garin Kaduna yayin da take kan aiwatar da wata gaggarumar aiki kamar yadda Air commodore Olatokunbo Adesanya ya sanar.