Ga muhimman batutuwa da shugaba Buhari yayi jawabin shi na murnar shiga sabuwar shekara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi cike da bayanai masu gamsarwa ga yan Nijeriya.
A cikin jawabin mai tsawo shugaban yayi magana akan nasarori da gwamnatin shi ta samu tare da shirin da suke yi na tarban sabon shekara.
Ga takaitaccen labarin abubuwa 7 da muka gano daga cikin jawabin shugaban na shiga sabuwar shekara:
1. Buhari yace zai saka wanda daya da wadanda suka haifar da wahalar reshin man fetur
Game da batun wahakar mai da ake fama da ita a kasar shugaban ya nuna bacin ran sa kan wahalar wanda ta sanya yan kasar cikin mawuaciyar hali yayin da ake bukuwar kirismeti da murnar shiga sabuwar shekara.
Shugaba Buhari yana inkari cewa wahalar mai da aka samu aniyar ce na yan kasuwa wajen yin butulci.
Shugaban dai yace ba zai lamunta da ire-iren hakan ba.
2. fannin samad da wutar lantarki ya bunkasa a kasar
Shugaban yayi amfnin da wannan damar wajen sanar da yan kasar nasarar da gwamnatin shi ta samu a bangaren samad da wutar lantarki.
An samu megawat 7,000 kuma a ranar 8 ga watan disamba kasar ta samu megawat 5,155 ga masu amfani da lantarki wanda wannan shine yawa da aka samu a tarihi, inji shugaban.
3. Sauya fasalin kasa ba shi bane matsala amma hanyar samad dashi shine babban matsala
Game da cece-kuce da wasu yan Nijeriya keyi kan sauya fasalin kasa musamman daga yankin kudancin kasar, shugaban ya kara aske gamne da batun.
Shugaba Buhari yace yana sane da batun kuma babu yadda za'a cinma burin haka idan har ba'a samu cigaba a fannin kasuwanci da walwala.
Yace shidai nashi ra'ayi game da batun shine wahalar da kasar ke fama da ita shine kan gaba ba sauya fasali ba.
4. Yan siyasa na amfani da addini da kabilanci wajen haifar da rikici
Shugaban yace yayin da lokacin zabe ke gabatowa ya kamat yan siyasa su daina amfani da addini ko kabilanci dake haifar da rikici idan har suna son kasar ta samu zaman lafiya.
Ya bada misali ga jihohin gabashin kasar yanda suka wanzar da addini da kabilanci da siyasa domin samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Karanta >> Ko dai shugaba Buhari ya fara yakin neman zabe?
5. Shigowa da shinkafa daga kasar waje zai tsaya bana
Shugaba Buhari yace shekara 2018 shine shekarar da kasar zata daina shigowa da shinkafa daga kasar Thailand, Indonesia, Philipines da dai sauran su.
A bisa bayanin shugaban, harkar noma ta samu cigaba kuma daga bana yan Nijeriya zasu cigaba da amfanin da shinkafa wanda aka nome a kasar.
6. Za'a canja akalar zuwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa
Shugaban yace gwamnati na bakin kokarin su wajen bunkasa harkan kasuwanci.
Bugu da kari shugaban yace an fidda sabbin shirye-shirye da tsarurruka da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
7. Shugaban yana mai matukar farin ciki game da addu'o'in da aka yi masa
Bayan ya kwashi ranaku 100 yana jinyar rashin lafiya a kasar waje cikin 2017.
Shugaban ya nuna farin ciki ga yan kasar tare da yin godiya kan addu'o'i da aka yi masa.
Shugaban yace a shirye yake yanzu wajen tafiyar da alamuran shugabancin kasar.