Sanata Isa Misau: Ministan Buhari na kulle-kulle wajen ganin an tsige Bukola Saraki daga mukamin shi - Inji Sanata

Sanata Misau

Dan majalisar mai wailtar jihar Bauchi yace kulle-kulle ya faru ne tun lokacin da aka tafi hutun kirismeti da ta sabuwar shekara.

Dan majalisar dantawa Isa Misau yana zargin wani ministan shugaba Buhari da yin bita-da kulli domin a tsige shugaban majlisar datawa Bukola Saraki daga mukamin shi.

Sanata Misau yayi wannan korafin yayin da yake bayani a zauren majalisar dokoki ranar laraba 17 ga watan janairu 2018.

Dan majalisar mai wailtar jihar Bauchi yace kulle-kulle ya faru ne tun lokacin da aka tafi hutun kirismeti da ta sabuwar shekara.

"Sanda muka tafi hutu wasu mutane sun yi kokari tsige shugaban  majalisar dattawa a bayan fage."ya bayyana a zauren.

*Uwargidan shugaban kasa ta mayar da martani bisa ga zargin da dan majalisa yayi

Sanata Misau yace dalilin da ya sanya ake kokarin tsige shugaban shine don ana sa ran cewa zai sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP.

Ciki bacin rai yana mai cewa; "a lokacin hutun, wani minista yake jagorantar wannan yunkurin. Dalilin shi shine don ana sa ran cewa shugaban majalisar zai fice daga APC don haka suke ganin cewa ya kamata su janyo masa matsala. Shin wani irin kasa ne wannan? komai sai a danganta ta da adini ko kabila.

 

Yace an nada wasu ba tare da sun cancanta ba

Hakazalika Sanata ya tofa albarkacin bakin shi game da nada wasu mutane wadanda basu cancanta ba a wasu ma'aikata masu muhimmanci.

"Mafi yawancin mukamai da gwamnatin nan ta bayar ba bisa cancanta aka bayar dasu. Wasu mutanen sun mamaye ayyukan gwamnatin kamar sun fi shugaban kasa wajen bada umarni" ya kara.

Dan majalisar wanda a baya yayi fito-na-fito da sufeto yan sanda kan zargin yi ma hukumar jami'an tsaro zagon kasa ya nuna bacin ran sa game da yadda harkar shiri'a ke wakana a kasar duk da cewa gwamnatin na takama da taken yakin kawar da cin hanci da rashawa a kasar.

*Dan majalisar dattawa zai amsa tambayoyi game da zargin da yayi ma sufeton yan sanda na kasa

Sanatan ya soki babban alkalin kasa

Yace wadanda basu aikata laifin rawan gani ake gurfanar dasu a gaban kotu amma masu manya-manyan laifuffuka suna har yanzu ba hukunci da aka zantar masu.

Misalai da sanatan ya bayar game da rashin adalci a harkar shari'a shine batun tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda kwamitin mataimakin shugaban kasa suka kama da laifi tare da takaddamar tsohon shugaban kwamitin gyaran fuska na hukumar fansho Abdulrasheed Maina wanda babban alkali na kasa ke kokarin hana a tuhume shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post