Rikicin kwankwasiya da Gandujiya: An kafa kwamitin tsaro game da zuwan kwankwaso jihar Kano

anyi sare-sare tsakanin yan kwankwasiyya da Gandujiyya

Ministan ayyukan cikin gida Janar Abdurahman Dambazau mai ritaya zai jagoranci wannan kwamitin tare da saura manyan sojoji da yan sanda masu ritaya

An nada sabon kwamitin wanda zata tabbatar da tsaro zuwan tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattawa Engr.Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso zai gudanar da taro ne ga mabiyan sa ranar 30 ga wata janairu.

*Hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Kwankwaso

Babban ministan ayyukan cikin gida Janar Abdurahman Dambazau zai jagoranci kwamitin.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Dokta Danyaro Ali Yakasai, wanda shi ne mataimakin shugaba da Munir Dahiru a matsayin sakatare. Sai Kanal Garun-Malam mai ritaya, da Janar Ahmad Tijjani Jibril mai ritaya, da Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, da mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda Bala Abdullahi mai ritaya da sauran manyan hafoshin ‘yan sanda da sojoji masu ritaya.

A bayanin daya daga cikin yan kwamitin Alhaji Sunusi Surajo Kwankwaso an kafa kwamitin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da ziyarar cikin kwanciyar hankali da lumana kuma ya yi alkawarin cewa za su gudanar da taron cikin lumana.

Rikicin Kwankwasiya da Gandujiya

Tun ba yau ba ake halin kare jini-biri jini tsakanin magoyan gwamna Ganduje da yan kwankwaso.

A makon da ya gabata magoyan yan siyasar sun shiga halin hargatsi a wata daurin aure da aka gudanar a nan garin Kano.

Haduwar su ke da wuya sai gashi tayi sanadiyar raunata jama'a da dama ciki har da danuwan kwamishnan ayyuka ta musamman wanda ke mara ma kwankwasiya baya.

 

Duk a kan wannan hargitsin da ya faru tsakanin yan kwankwasiya da Gandujiya rundunar yan sanda na jihar Kano ta sanar cewa ta kama yayan kwamishnan wato Abbas Abdullahi Abbas da Sani Abdullahi Abbas bisa ga zargin laifin tayar da tarzomar.

*Gwamna ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa Ibro da kayan daki

Kalaman Kwamishnan ayyuka ta musamman

A baya dai cikin wani faifan bidiyon da yayi yawo a duniyar gizo, kwamishnan ayyuka ta mussaman wato Abdullahi  Abbas Sanusi yayi wasu kalaman tunzura wadanda ake zargin su suka haifi tarzomar tsakanin mabiyan akidojin.

Bisa ga wannan zargin kwamishnan yan sanda na jihar Kano ya tura ma kwamishnan tsammaci kan yazo ya bayyana dalilai da ya sanya ya furtar da kalaman.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post