Rikicin BUA da DANGOTE: Yan fashi sun kai wa tawagar gwamnan Edo hari

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki

Ana neman wasu masu ruwa da tsaki na kamfanin BUA ruwa a jallo dangane da harin da aka kai ga tawagar gwamnan

wasu yan fashi sun far ma tawagar motocin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki jihar a wata takarda da kakakin gwamnan  ya fitar ranar ALhamis 4 ga watan Janairu.

Kakakin Robin Crusoe ya sanar cewa yan sanda suna neman  wasu masu ruwa da tsaki na kamfanin BUA siminti dake nan Obu ruwa a jallo domin ana zargin cewa suna da hannu wajen aiwatar da farmakin da aka kai wa tawagar gwamnan.

Tun ba yau ba ake kai kawo tsakanin kamfanin BUA da Dangote game da mallakar wani filin tonon ma'adanai dake nan Okpella a jihar Edo.

 

Gwamnatin jihar ta umarci kamfanin da ta dakatar da aikin a filin amma kamfanin taki lamunta da umarnin.

Ranar laraba 3 ga wata janairu ne tawagar gwamnatin jihar ta ziyarci filin tare da jami'an tsaro har suka kama wasu ma'aikatan BUA guda 2 bisa ga rashin bin umarni da aka basu na daina aiki a filin.

A sanarwar da kakakin ya fitar, Crusoe ya fitar cewa yan sanda na zargin shugaban BUA Binji da saka hanu kan harin da aka kai wa gwamnan.

Bisa labarin da takardar ta kunsa, tun ba yau ba aka kaddamar da Binji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa ga labarin da jami'an tsaro suka samu mai cewa kamfanin BUA tana bayar da gudummawa ga wasu yan tsegeru a nan Okpella inda kamfanin siminti da filin tonon ma'adanai na kamfanin yake.

Ana sa ran cewa tsegerun suka gudanar da harin da aka kai wa gwamna.

Post a Comment

Previous Post Next Post