Shugaban kungiyar ya nuna bacin ran sa game da matakin da takwarar shi Isma'il Na'abba Afakallahu na hukumar tace finai finai ya dauka na yafe ma jarumar.
Kungiyar masu shirya fina-finai hausa MOPPAN bata yarda da dawowar jaruma Rahama Sadau da yin fim ba duk da matakin da hukumar tace fina-finai tayi na yafe mata.
A labarin da BBC ta fitar, Shugaban kungiyar MOPPAN Alhaji Kabiru Maikaba yace kungiyar bata yarda a dawo da Rahama Sadau.
Matakin da shugaban tace fina-finai na jihar Kano ya dauka
A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar tace fina-finai na jihar Kano Alhaji Ismail Na'abba Afakallahu ya sanar cewa kungiyar ta yafe ma jarumar kuma zasu cigaba da tantance fina-finai ta.
Kan matakin da Afakallahu ya dauka, shugaban kungiyar MOPPAN yana mai cewa "Ai baya da hakkin gafarta mata don ba shi ya kore ta, mu muka kore ta. Shi yayi mana endorsing ne yace ya ji dadin korar da muka yi mata kuma ba zai sake duba fina-finan ta ba. Saboda haka don menene a yanzu daga baya don wani abu ya hada su zai je kawai yace ya dawo da ita.
Dalilin da yasa na karfafa gwiwan Rahama sadau wajen bada hakuri
Alhaji Maikaba yace matakin da Afakallahu ya dauka na duba fina-finai jarumar ba matsalar su bane don yane da yancin yin haka amma ya daina shiga cikin harkokin kungiyar su.
"wannan ba matsalar mu bane, yana da yancin duba fina finan ta. Amma mu kuma yana shigowa harkokin mu yana dagula mana lissafi cikin harkokin kungiyoyin mu. Don haka muka ce mu ba za yarba ba saboda irin abubuwan da yake yi don haka mu zamu dauki matakai muma saboda ya daina shiga cikin harkokin kungiyoyin mu ,Yace.
Damar kare kanta kan abubuwan da ta aikata
Shugaban yace a da dai sun kori jaruma amma ganin yadda mutane ke magana a kan hakan bayan ta nemi a gafarce ta yasa suka ce zasu saurari ta.
A cewar shugaban, sun yi kokari domin tattaunawa da Rahama a kan batun amma ta kiya. Daga baya sai ta tura masu sakon neman gafara. Bayan sun zauna da yan kungiyar kan wasikar da ta tura sai suka kira ta kan batun amma ta sanar masu cewa bata kasar, tana kasar Cyprus tana karatu. Dalilin haka suka aje takkadamar har sai bayan ta dawo don fadin abubuwa n da suke ganin tayi da ba dai dai ba domin ta kare kanta.
Alhaji Maikaba ya bada sharudan da zasu bi wajen sauraron ta kana su dau mataki a kan ta.
"Idan ta dawo, muka zauna da ita akwai takardu da muka shirya zata sa mana hannu. Akwai ja mata kunne da zamu yi kuma daga karshe zamu san matakin da zamu dauka akan ta.
Dakatarwa da aka yi mun ya bude mun kofofin samun nasara
Dangane da matakin da kungiyar ta dauka na korar ta daga masana'antar.
"Hakika ko Ubangiji kayi masa laifi ka tuna zai yafe maka amma yayin da kayi ka sake komawa kayi kuma ka sake komawa toh ko a wajen Ubangiji akwai kurewar tuban ka. Wannan yarinyar duka duka bata dade a cikin industry dinnan ba. Duka duka tayi shekara hudu ne amma a cikin shekara hudu abubuwan da tayi cikin industry din ko mutum da yayi shekara ashirin ko talatin ba wanda yayi shi, toh wa yasan abun da zata tinkimo mana nan gaba?".