Rahama Sadau: Bayan gafarar da ta nema, hukumar tace fina-finai ta yafe ma jaruma

Shugaban hukumar tace fina-finai Ismaila Na'abba Afakalla

Shugaban yace an dauki matakin ne bayan gafarar da jarumar ta  nema kwanan baya.

Hukumar tace fina-finan hausa ta yafe ma fitacciyar jaruma Rahama Sadau bisa laifin da ta aikata wanda yayi sanadiyar har aka dakatar da ita da yin fim.

 

Shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakalla ya shaida wa wakilin BBC haka.

Shugaban yace an dauki matakin ne bayan gafarar da jarumar ta  nema kwanan baya.

"Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al'umar da take ciki.

"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi".

Afakallah ya sanar cewa "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".

Dalilin da yasa na karfafa gwiwan Rahama sadau wajen bada hakuri

Jaruma ta bada hakuri

Rahama Sadau ta nemi gafara ne bisa kuskuren da tayi na rungumar wani mawaki a cikin bidiyon wakar shi.

A cikin watan Octoba na bara Fitacciyar jarumar ta bada hakuri ga gwamnan jihar kano da mai martaba sarkin kano da mabiyan fina-finan kannywood ne a wata hira ta musamman da tayi a shirin "ku karkade kunnuwan ku" wanda gidan rediyo na Rahama dake nan jihar Kano ke gabatarwa.

 

A cikin jaruman Kannywood ina son inyi aiki tare da Rahama Sadau- Inji fitacciyar jarumar Nollywood

Bayan haka ta tura wasikar neman gafara ga kungiyar wanda har sakataren kungiyar Muhammed Salisu ya tabbatar da isowar wasikar ga farfajiyar kungiyar. a cikin wasikar tana mai cewa;

"Ni halittar Allah ce wanda za ta iya aikata kuskure ko yaushe sannan kuma ni ‘ya ce mai laifi wanda ke shirin gyara abubuwan da nayi ba daidai ba. Ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu MOPPAN, da da masoya na da suyi hakuri da ni su yafe min" .

Yanzu haka jarumar tana kasar Cyprus inda take karatu kana tana kokarin fitar da wani sabon fim wanda ta dauki nauyin shiryawa mai take "Dan Iya".

Shirin wanda shine na biy da zata dauki nauyin fitarwa bayan RARIYA zai fito nan ba da jimawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post