Mohamed Salah: Dan wasan Egypt ya lashe kyuatar gwarzon shekara na nahiyar kasashen larabawa

Mohammed Salah

Salah yana kan gaba wajen samun kyautar gwarzon shekara ta nahiyar Afrika wanda za'a gudanar da bikin a kasar Ghana ranar Alhamis.

Shahararen dan wasan kungiyar Liverpool da tawagar kasar Masar Mohamed Salah ya samu nasarar zama gwarzon dan wasa na 2017 na yankin kasashen larabawa.

Ya samu kyautar bayan zaben da yan jarida masu fitar da labarun wasannin motsa jiki su 100 daga kasashen yankin larabawa suka yi.

Salah mai shekaru 25 ya taka rawan gani bana tunda ya sauya sheka daga AS Roma zuwa Liverpool wanda ya samu damar sanya kwallaye 17 a gasar firimiya.

Karanta >> Sallah ya nuna farin cikin sa samun kyuatar gwarzon dan wasan nahiyar afrika ta BBC

Ya taimaka wajen ganin kasar shi Egypt ta tsira a wassanin share fage na gasar cin kofin duniya.

 

Yan wasan kasar Syria Omar Khribin da Omar Al-soma suka biyo bayan a gasar zama gwarzon dan wasan nahiyar larabawa.

Sallah shine mafi farin jini wajen samun kyuatar gwarzon dan wasan nahiyar Afrika wanda za'a fitar ranar alhamis a bikin gasar wanda za'a gudanar a birnin Accra babban birnin kasar Ghana.

Post a Comment

Previous Post Next Post