Majalisar dokoki: Haya-gaga a zauren majalisar dokoki yayin da wani dan majalisar ke neman sauya sheka zuwa APC

Zauren majalisar dokoki na kasa

Dan majalisar ya sanar cewa bisa ga wasu dalilai na rashin gamsarwa dake wakana a cikin jam'iyar PDP na jihar tashi har ma da ta kasa baki daya ya sanya zai barta zuwa jam'iyar adawa.

An samu wani tashin hankalin a zauren majalisar dattawa yayin da wani dan majalisar ya sanar da ficewar shi daga jam'iyar PDP zuwa ta adawa ta APC.

A zaman da yan majalisar suka yi ranar laraba 17 ga watan yau, sanata Sonny Ogbuoji mai wakiltar jihar Ebonyi ya tashi tsaye a zauren domin sanar cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

*Kalli hotunan yan majalisar dokoki yayin da suke motsa jiki a filin kwallo

Dan majalisar ya sanar cewa bisa ga wasu dalilai na rashin gamsarwa dake wakana a cikin jam'iyar PDP na jihar tashi har ma da ta kasa baki daya ya sanya zai barta zuwa jam'iyar adawa.

Wannan sanarwar bata yi ma sauran yan jam'iyar PDP dadi ba inda suka nemi shi da ya dakatar da yin haka har sai ya shawarci yan jam'iyar.

Bisa ga wannan yunkurin suma yan APC dake zauren suka bukaci shi da ya cigaba da aniyar sa.

*Yan jam'iyar PDP na majalisar wakilai sun nuna rashin jituwa ga kakakin majalisa

Bayan mintuna 15 da yin nazari dan majalisar ya dakatar da sanarwar tashi har sai bayan ya tuntubi yan jam'iyar PDP.

Post a Comment

Previous Post Next Post