Lawal Kaita: Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita ya rasu

Tun ranar laraba shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa sakon ta'aziya ga iyalin marigayin

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a jamhoriyar ta biyu Alhaji Muhammad Lawal Kaita ya rasu jiya Talata 2 ga watan farko na sabuwar shekara ta 2018.

Marigayi Kaita ya rasu yana da shekaru 85 a duniya ranar talata a wata asibiti dake birnin tarayya bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Babban dan dan marigayi Alhaji Abubakar Lawal Kaita ya sanar da mutuwar mahaifin su.

A cewar sa za'a yi janaizar shi a garin Katsina safiyar ranar laraba 3 ga watan Janairu.

An haifi Lawal Kaita reanar 4 ga watan Octoba na 1932 a garin Katsina.

Karanta >> Shugaban ƙasa yana jimamin rasuwar Kanti Bello

An zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kaduna zamanin jamhoriyar ta biyu karkashin jam'iyar NPN tsakanin watan Octoba da Disemba na 1983.

Marigayi ya rasu ya bar uwardakin shi da yara har da jikoki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalen shi tare da yi masa addu'ar Allah ya jikan shi da rahama.

Post a Comment

Previous Post Next Post