Ke duniya ina kika yi damu? Saurayin da yayi ma kajin makwabcin shi fyade har suka mutu

Chesoni ya aikata wannan mummunar aikin ga kajin makwabcin shi

Bayan ya aikata mummunar aikin har washe garin safe aka cafke shi yayin da yake kokarin neman yadda zai boye matattun kajin.

Garin Kaptwen dake gundumar Bomet County na kasar Kenya sun tashi da hayaniya yayin da al'ummar garin suka kama wani mutum wanda yayi ma kaji biyu fyade har tayi sanadiyar mutuwar su.

Mai laifin Alfred Kipkemoi Mutai wanda aka fi sani da Chesoni dan shekara 33 ya aikata laifin ne bayan ya saci kajin daga harabar makwabcin shi a daren ranar asabar 20 ga watan janairu.

Bayan ya aikata mummunar aikin har washe garin safe aka cafke shi yayin da yake kokarin neman yadda zai boye matattun kajin.

Shi dai wannan bawan Allah ya ji ba dadi daga hannun jama'a bayan ya amsa laifin tuhumar da suka yi masa na ya bayyanar masu inda ya nufa da matattun kajin.

Bayan dukar da ya sha daga al'ummar gari, sai suka umarci shi da ya biya diya.

Shi dai ainihin mai kajin Richard Kibor Tonui ya sha alwashi cewa sai an biya shi Ksh4,000 kudin kasar Kenya kana zai gafarta ma laifin.

Daga karshe wannan saurayi wanda aikata wannan aikin ya dau alkawarin yin aure domin samu ingantaccen rayuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post