Kwanan baya labari ya fito tare da hotunan kayan lefe da aka kai gidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje bayan neman aure da dan gwamna jihar Oyo yayi ga diyar shi.
Wani saurayi ya nuna bacin ran sa game da yadda mata suke ta tsokaci ganin hotunan kayan lefe da aka kaima diyar gwamnan jihar Kano Fatima Ganduje.
Kwanan baya labari ya fito tare da hotunan kayan lefe da aka kai gidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje bisa ga neman aure da dan gwamna jihar Oyo yayi ga diyar shi.
Abu ba'a cewa komai, kayan dai kamar yadda majiya suka shaida mana da tireloli aka sauke su. Kana an gudanar da wata biki domin karban kayan.
Sakamakon hakan jama'a da dama suka yi tsokaci game da wannan kayan da aka kai, cikin har da mata.
Wasu har suka fara kwallafa ma kansu cewa suma irin haka suke so idan har zasu yi aure. Wato sai mai naira.
*Gwamna ya tallafawa diyar marigayi Rabilu Musa Ibro da kayan daki
Bisa ga wannan, wani saurayi ya sako nasiha cikin faifan bidiyo ga ire-iren mata dake da ruwan ido akan kayan dukiya.
Wannan bidiyon nashi yana ta yawo a kafafen sada zumunta inda jama'a da dama nata gasgata sakon da ya fitar tare da yaba mashi.
Mafi yawanci ma mata suka aikata hakan.