Ibe Kachikwu: Minista ya musanta zargin yunkurin kara kudin man fetur

Karamin ministan mai Ibe Kachikwu

Kakakin ma'aikatan mai yayi kira ga jama'a da suyi watsi da jita-jitan dake yaduwa na cewa gwamnati na kokarin kara kudin mai

Karamin ministan mai Ibe Kachikwu ya musanta zargin dake yaduwa na cewa gwamnati nayunkurin kara kudin man fetur.

A wata takarda da kakakin ma'aikatan mai Idang Alibi ya fitar ranar Alhamis 4 ga wata, ministan yayi bayanai kan karancin man fetur da aka samu a gaban yan majalisar dokoki.

"Ma'aikatar man tana kara jaddada ma jama'a cewa mai girma minista bai bayyanar da labarin yunkurin kara kudin man fetur" a cewar Alibi.

Kakakin ya kara bayana batutuwan da Ministan ya sanar ma yan majalisar zaman da yayi dasu a farfajiyar su wanda aka watsa a gidan telebijin ta NTA kai tsaye.

Minista yayi juyi kamar mazari cikin kayan gargajiya wanda aka yi da fatar damisa (bidiyo)

Alibi ya sanar cewa fadar shugabam kasa ta kaddamar da wata kwamiti wanda zata yi bincike akan abubuwan dake haifar da wahalar mai domin samun hanyar kawar da kalubalen.

Yayi kira ga jama'a da suyi watsi da jita-jita mai cewa na yunkurin kara kudin man fetur.

A zaman tattaunawa da Kachikwu yayi da yan majalisar dokoki ministan, ya bayyana ma yan majalisar cewa kamfanin man fetur ta kasa NNPC ta samu Naira biliyan 85.5 sanadiyar shigowa da mai daga kasar waje tare da sayar dashi akan farashin N145 kan lita daya tun daga  watan Octoba na 2017.

Post a Comment

Previous Post Next Post