Sakon juma'a tamu ta yau daga Falalu Dorayi
Ga sakon barka da juma'a daga babban direktan Kannywood Falalu Dorayi yau juma'a 26 ga wata janairu.
MU GUJI KAZAFI D A NEMO L A I F I N JUNA.
"Bai halatta ba ga Mumini, Ya ringa bibiyar yan uwansa Muminai domin ya gano NAKASUNSU da GAZAWARSU da AIBUNSU ko KAZANTARSU
Lallai haka mummunar dabi'a ce mai HALAKARWA.
Dabi'a ce ta mutanen da ake zargi, kuma KAZANTA ce, Kuma hakan ya sabawa shari’ar ALLAH MAI GIRMA, Ya sabawa koyarwar Annabi MUHAMMAD (SAW). RASULULLAH (SAW) Yace;: “Albarka ta tabbata ga wanda ya shagaltu da laifuffukansa daga laifuffukan mutane.”
Barka da juma'a.
Tags:
News