Gasar CAF Award: Yar wasan Nijeriya ta lashe kyuatar gwarzuwar shekara (Hotuna)

Asisat Oshoala

Manya-manyan yan wasa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallo sun halarci taron bikin gane gwarzayen nahiyar Afrika ta CAF wanda aka gabatar a Accra babban birnin kasar Ghana.

Yar wasan tawagar Super Falcon ta Nijeriya Asisat Oshoala ta lashe kyuatar gwarzuwa ta shekara a nihiyar Afrika ta gasar CAF.

Bayan Mohamed Salah na kasar Egypt ya lashe kyautar a bangaren maza ita ma yar kasar Nijeriya ta samu nata a bangaren mata a gasar karrama yan wasan nahiyar Afrika wanda CAF ke gabatrwa ko wace shekara.

 

Asisat wanda ke taka tamaula a kungiyar Dalian Quanjian ta kasar Sin ta take bayan Chrestina Kgatlana ta kasar Afrika ta kudu da Gabrielle Aboudi Onguene na kasar kamaru wajen samun nasarar samun kyautar.

Yar Nijeriya ta taka rawan gani komawan ta Dalian Quantian inda har ta taimaki kungiyar wajen samun nasarar cin babban kofin kasar Sin wasan wanda ta samu damar saka kwallaye 2 a ragar Shanghai wanda aka tashi 5-3.

Yar shekara 23 ta samu kyautar gwarzuwar shekara na kakar 2017 firimiya ta mata na kasar Sin.

FIFA ta sauya sakamakon wasan Nijeriya da Algeria tare da hukunta NFF na biyan diya

Wannan shine karo na uku da zata samu kyautar kuma tana kan gaba wajen wuce fitacciyar yar wasan Nijeriya Perpetual Nwakocha wajen samun kyautar.

 

Yanzu haka Asisat ta karbi kyautar sau uku yayin da ita Perpetual ta amshi kyautarhar sau Hudu.

Bikin gasar CAF na 2017

Manya-manyan yan wasa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallo sun halarci taron bikin gane gwarzayen nahiyar Afrika ta CAF wanda aka gabatar a Accra babban birnin kasar Ghana.

Tsohon dan wasan kasar Ivory coast da kungiyar Chelsea Didier Drogba da shahararen dan wasan fim ta masana'antar Hollywood Boris Kodjoe suka gabatar da bikin wanda aka gudanar a daren ranar Alhamis 4 ga watan janairu.

 

manyan baki da suka halarci bikin gasar sun hada da Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Ado, shugaban FIFA Gianni Infantino, shugaban CAF Ahmad Ahmad, matar sabon shugaban kasar Liberia kuma tsohon dan wasa Clear Weah, Samuel Eto'o, tsohon dan wasan Nijeriya Emmanuel Amunike da sauran su.

Yan Afrika 10 da suka fi amsar kudi a turai

Shahararrun mawaka Wizkid, Olamide, Tiwa Savage, Phyno, Flavour, Fally Ipupa da Effya suka nishadantar da baki a bikin wanda aka karrama tsohon zakaran gwajin dafi ta afrika kuma sabon shugaban kasar Liberia na yanzu wato George Weah.

Post a Comment

Previous Post Next Post