Martanin da gwamnan yayi kenan bisa yajin aikin da NUT ke yunkurin yi a jihar bisa korar malamai da gwamnatin jihar tayi.
Gwamnan jihar Kaduna Malama Nasir Elrufai ya sanar cewa duk wani malami da ya tafi yajin aiki wanda kungiyar malamai ta NUT ta yunkuro ya sani cewa yin haka zai haifar da sallama.
Martanin da gwamnan yayi kenan bisa yajin aikin da NUT ke yunkurin yi a jihar bisa korar malamai da gwamnatin jihar tayi.
Gwamna yayi wannan korafi a shafin sa na tuwita yau 8 ga wata. yana mai cewa,
Yayan talakawa ke zuwa makarantar firamare na gwamnati a jihar Kaduna. Hakkin mu ne mu samar masu ingantaccen ilimi kuma muna kan yin haka.
Babu abun da zai hana mu sallamar malamai 22,000
Duk wani malami dake sa ran bin NUT shiga yajin aiki, su sani cewa idan sunyi haka zasu fuskanci hukunci sallama daga aiki.
Gwamnan dai yace bazasu lamunta da cin fuska.
Tags:
News