El-zakzaky: Yan Shi'a da jami'an tsaro sun gwabza a garin Abuja

Shugaban darikar shia'a na Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky

Yan sanda sun kama mabiya 52 tare da makami yayin da suka zanga-zanga

Jami'an yan sanda da mabiyan darikar Shia sun gwabza a garin Abuja ranar laraba 10 ga watan farko na 2017.

Jami'in sun gamu da mabiyan kungiyar Islamic movement of Nigeria yayin da suke zanga zanga kan a saki jagoran su Ibrahim El-zakzaky wanda ke garkame a hannun jami'an tsaro.

Lamarin ya faru ne a titin Moshood Abiola dake Area 2 jim kadan bayan mabiyan sunyi tattaki daga yankin Garki na birnin tarayya.

*Gwamnatin jihar Kaduna tayi kashedi ga yan darikar shi'a kan yi wa zaman lafiya barazana

A  bisa rahoton da jaridar Premium times ta fitar, yan kungiyar sun bukaci jami'an yan sanda da su basu damar cigaba da zanga-zanga cikin zaman lafiya. Basu samu damar cinma bukatar da suka nema ba inda aka kai masu farmaki da barkonon tsohuwa tare da yin harbin tsorotarwa.

Kwatankwacin hakan ya faru kwanan baya yayin da mabiya suka kai koken su farfajiyar majalisar dokoki.

Sakamakon gwabzawa

Kan zanga-zangar da suka yi, wasu mabiyan darikar shiá sun shiga hannun hukuma.

A wata takarda da kakakin yan sanda DSP Anjuguri Manzah ya fitar, an kama mabiyan kungiyar su 52.

Kakakin yace an kama su ne tare da kunshi bam karar irin ta gargajiya da duwatsu har ma da gwafa.

 

Dalilin kama El-zakzaky

Shekara biyu kenan da ka garkame jagoran yan Shia Ibrahim El-zakzaky bayan harin da rundunar sojoji suka kai mashi a gidan sa dake Zaria wanda yayi sanadiyar kashe daruruwar mabiyan shi ciki har da yaran sa guda uku.

Sojojin sun yi hakan ne sanadiyar gwabzawar da mabiyan darikar suka yi da tawagar hafsan sojoji na kasa janar Tukur Buratai

Duk da cewa babban alkali Gabriel Kolawole ya zantar da hukunci na a sake shi cikin watan Disemba na 2016, har yanzu shugaban yana hannun hukuma tare da matar shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post