Don Wani: Gwamnatin tarayya ta rusar da katafaren gidan gawurtacen dan ta'adda

Ginin kenan kafin a rushe

Gidan kirar irin ta zamani kuma wanda aka gina da miliyoyin kudin ya koma fili sanadiyar dandazo da masu rushe-rushe suka yi ma ginin

Gwamnatin tarayya ta rusar da katafaren ginin gidan gawurtacen dan ta'adda Igwedibia Johnson wanda jami'an tsaro suka kashe kwanan baya a jihar Enugu.

 

A rahoton da jaridar Punch ta fitar, an rusar da ginin har ta koma fili sanadiyar dandazo da aka yi ma ginin ranar 9 ga wata 2018.

Shekau ya fitar da sako a cikin faifan bidiyo (Bidiyo)

 

A bisa labari jami'an tsaro sun garwayen harabar ginin domin tabbatarb da tsaro yayin da masu aiki ke iya bakin kokarin su wajen kurmushe ginin.

General Don wani kamar yadda aka fi sanin shi dashi ya gamu da ajalin shi ne yayin da gamayar sojoji da yan sandan farar hula suka kai mashi harin bazata a jihar Enugu.

Don waney mai shekaru 34 yana daya daga cikin tsegerun Neja delta dake addabar al'umma a yankin kudancin kasa.

Rahotannin sun nuna cewa shi ya gudanar da hari ranar murnar shiga sabuwar shekara a wata coci dake Omoku na jihar Ribas wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 17.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post