Daukan mataki mai tsauri kan dalibai: Gwmnati jihar nasarawa ta hukunta malamai bisa zana yara da suka yi

Ana dab da daina daukan mataki mai tsauri kan dalibai a Nijeriya

A cikin bidiyon wanda yayi yawo a duniyar gizo an gan inda wani malami ke dukar dalibai da bulala bisa laifin rashin komawa makaranta da wuri bayan hutun karshen sashe da aka yi.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta hukunta shugaban makarantar kimiya dake Nasarawa-Eggon tare da malamai uku bisa zana yara da ya faru a mkarantar wanda har ta zagaya kafaffen sada zumunta.

A cikin bidiyon wanda yayi yawo a duniyar gizo an gan inda wani malami ke dukar dalibai da bulala bisa laifin rashin komawa makaranta da wuri bayan hutun karshen sashe da aka yi.

 

*Duk malamin da ya tafi yajin aiki, ya sani cewa iya bakin aikin sa kenan

Kwamishnan ilimi na jihar Ahmed Tijjani ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta hana a daukan hukunci mai tsauri kan yaran makarantun gwamnati dake fadin kananan hukumomi 13 dake jihar.

Hirar shi da manema labarai ranar akhamis 18 ga wata Janairu, Ahmed ya sanar cewa shugaban makarantar da lamarin ya faru tare da ma'aikatan makarantar sun samu hukuncin dakatarwa na wata daya kana bayan haka an kafa kwamiti wanda zata yi bincike kan lamarin.

Kwamishnan ya sanar cewa ma'aikatar ilimi na jihar ta tura wasika zuwa makarantu kan hana daukan mataki mai tsauri ga yara dalibai.

Daga karshe kwamishnan ya ja kunnen malamai game da daukar irin wannan mataki nan gaba domin duk wanda aka kama da yin hakan zai fuskanci hukunci horo mai tsanani.

Post a Comment

Previous Post Next Post