Dakingari yace bayan nazarin da yayi bayan kusan shekara uku da sauka mukamin gwamna ya yanke hukuncin komawa APC
Tsohon gwamnan jihar Kebbi Alhaji Usman Dakingari ya jagoraci daruruwan mabiyan shi sauya sheka daga jam'iyar PDP zuwa APC.
Da hannu biyu shugaban jam iyar na jihar Kebbi Alhaji Attahiru Maccido ya karbe su a bikin taro wanda aka gudanar a filin wasa na Halliru Abdu dake nan Birnin Kebbi ranar asabar 20 ga wata.
A jawabin shi, tsohon gwamnan ya bayyana cewa bayan nazari da yayi na tsawon shekara 3 da barin kujerar gwamna ya yanki shawarar komawa APC bisa yadda shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kebbi na yanzu Alhaji Atiku Bagudu ke gudanar da alamuran shugabanci cikin tsari.
"Cikin tsawon shekara uku babu wanda yaji murya ta a harkara siyasa kuma na dawo jam'iyar APC ne ba don wata manufa daban ba sai dai don irin rawar da Shugaba Buhari da Atiku Bagudu suke takawa wajen samad da cigaba da zaman lafiya." inji tsohon gwamnan.
Ya kara da cewa"ina kira ga duk wanda nayi masa laifi da ya gafarce ni kuma nima na gafarta ma duk wanda yayi mun laifi.
A nashi jawabin, gwamna Atiku Bagudu yayi ikirari cewa jihar zata cigaba da samun nasara idan ire -iren daruruwan mutane suna dawowa inuwar jam'iyar APC.
Shima shugaban jam'iyar reshin arewa maso yamma Alhaji Inuwa Abdulkadir ya yaba ma sabbin shiga bisa matakin da suka dauka na dawowa jam'iyar APC.
Cikin wadanda suka koma jam'iyar APC tare da Dakingari akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Rabiu Kamba da tsohon dan majalisar wakilai na tarayya Alhaji Sani Kalgo tare da Abdullahi Dan-Alkali da Alhaji Haruna Hassan da Halima Tukur.