Buhari: Yan Nijeriya zasu cire Buhari daga kujerar shi a zaben 2019 - Reveren Mbaka

'Nigerians will vote you out in 2019,' Fr. Mbaka tells President

Mbaka yace gwamnatin Buhari ta sanya mutane shiga yanayin kuncin rayuwa

Babban limamin cocin katolic reveren Ejike Mbaka yace yan Nijeriya zasu cire shugaba Buhari a karagar mulkin kasa a zaben 2019 idan har ba'a samu kakkwarar canjin yanayi a kasar.

Reveren Mbaka wanda shine babban limamin cocin Adoration ministries dake nan jihar Enugu yayi wannan gargadin yayin da yake jawabin daren washegarin ranar shiga sabuwar shekara.

Yayi tsokaci kan yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanya mutane shiga matsananciyar hali ta kuncin rayuwa tare da jaddada ma shugaban da yayi hanzari wajen wanzar da matsaloli da yan kasar ke fuskanta.

A bayanin sa muhimmin silar wahalhalu da yan kasar ke fuskanta daga bangaren kasuwanci ne kuma idan har shugaban bai kawo canji yan Nijeriya zasu canja shi a zaben 2019.

Limamin  ya yaba kyakyawar halayen shugaban inda ya kara da cewa shugaba Buhari mutumin kirki ne amma yana zaune ne tare da wasu miyagun mutane.

Karanta >> Tsarin dimokradiya ke hana ni hukunta masu aikata laifi

Shawarar shi ga yan Arewa

Ya baiwa yan  Arewa shawarar tsayar da dan takara kafin zaben 2019.

Ya bada shawarar na a tsayar da gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo domin ya maye gurbin shugaban. A cewar shi gwamnan yana kokartawa wajen aiwatar da ayukan cigaba a jihar shi.

A cikin 2014 Mbaka yayi makamancin irin wannan wahayi idan ya sanar cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai fadi a zaben 2015 kuma Shugaba Buhari zai maye gurbin shi. Hakan dai ya faru zahiri don har yanzu shugaba Buhari shine a kan karagar mulkin kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post