Buhari: Dalilin da ya sanya matattu suka samu mukami

Shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya tace bai kamata jama'a su kushe ta ba dangane da nadin da tayi na wasu ma'aikata wanda cikin jerin sunayen akwai matattu.

Fadar shugaban kasa ta bayana dalilin da ya sanya aka samu sunayen matattu cikin jerin sunayen wadanda aka nada mukamai a wasu ma'aikata da majalisu.

A ranar juma'a 29 ga wata ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da nadin wasu masu ruwa da tsaki 209 da wasu membobi 1258 a ma'aikata daban daban.

A jerin sunayen wanda babban sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya fitar ciki akwai sunayen wasu matattu.

Wannan lamarin ya janyo tsegumi tsakanin yan kasar inda jama'a ke kushe gwamnatin Buhari.

Dangane ga batun fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sanya aka samu sunayen matattun cikin jerin sunayen.

A jawabin da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya fitar, an samad da sunayen ne tun ciki 2015 lokacin shugaban kasa ya umarci jam'iyar APC na ko wace jiha da ta fitar da sunayen mutum 50 da za'a baiwa mukami a ma'aikata daban daban.

 

Karanta >> Har yanzu Yusuf na jinya a Nijeriya, bai tafi kasar waje

Bayan an samu sunayen wanda tsohon sakataren gwamnati Babachir Lawal ya hada su cikin 2016 an samu komawa baya tsakanin wasu gwamnoni inda suka cewa ba da izinin su aka fitar da sunayen ba.

Dalilin haka shugaban ya kafa wata kwamiti domin tantance sunayen wanda shi mataimakin shi Yemi Osinbajo ya jagoranci kwamitin. Kwamitin ta hada da gamayyar wasu gwamnoni da manyan manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC a matsayin membobi.

Tafiyar Shugaban zuwa neman lafiya jikin sa ya dakatar da lamarin. Shehu ya kara da cewa a kwanan nan ne shugaban ya tuna da batun.

"Bisa ga umarni ne sakataren gwamnati tarayya ya fitar da sunayen ba tare da ya lura ko yayi gyara cikin ta ba ya fitar dashi. Inji Shehu.

SHehu ya kara da cewa babu wani abun tashin hankali tare da sunayen kuma za'a sauya sunayen matattun da wasu daban.

Kuskure ne aka samu kuma babu dan Adam da baya rabuwa da tafka kuskure inji kakakin shugaban.

Post a Comment

Previous Post Next Post