Boko haram: Sojoji sun samu motocin yaki daga kamfanin Innoson dake Nijeriya

Innoson supplies Army with vehicles to fight Boko Haram

A cikin yarjejeniya da rundunar sojoji suka kulla da kamfanin, Innoson zata kirkiro kayan aikin sojoji da motocin yaki

Rundunar sojoji dake fafitikar yakar yan boko haram ta samu sabbin motoci daga kamfanin kirar mota ta Innoson domin cigaba da yunkurin da suke yi.

Wannan yana daga cikin yarjejeniyar da sojoji suka kulla da kamfanin wajen kirkarar kayan aikin sojoji da motocin don amfanin runduna wajen yakar Boko haram.

Wannan ya fito ne ranar litinin 15 ga wata daga hukumar sojoji. bisa takardar da aka fitar an gabatar da motocin ga dakarun Operation lafiya Dole dake yakar boko haram a arewa maso gabas.

Kulla yarjejeniya

A kwanan baya ne babban hafsan sojojina kasa janar Tukur Buratai ya sanar cewa sojoji zasu kulla yarjejeniya da kamfanin Innoson wajen kirar kayan aikin sojoji da mota.

kamfanin dai ta kaddamar da motoci 40 ga sojoji a kwanan baya wanda dashi dakarun operation lafiya dole ke  zirga-zirgar yaki dashi.

A cewar babban hafsan, motocin da kamfanin ta kera kwanan ya tabbatar masu cewa zata iya kirkirar motocin yaki ma sojoji musamman wadanda zasu iya juriya a yankin arewa maso gabas.

Post a Comment

Previous Post Next Post