Boko haram: Shekau ya fitar da sakon a cikin faifan bidiyo (Bidiyo)

shekau da tawagar sa

Yace kungiyar tana nan lafiya kuma babu jami'an tsaro da zasu hana sukaurace daga bakan su

Shugaban kungiyar ta'adda ta Boko haram Abubakar Shekau ya sake fitar da wani sakon bidiyo a jiya talata 2 ga watan janairu.

Wannan shine karo na farko da shugaban kungiyar zai fitar da sako ga jama'a bayan ya kwashi kwanaki da dama bai yi hakan ba.

A cikin sakon da ya fitar, Shekau yana tabbatar ma jama'a cewa wannan sakon gaisuwa ne kuma suna nan lafiya babu abun da ya same su.

Karanta labarin>> Abubuwa 7 da wani kwamandar Boko haram ya bayyanar game da kungiyar

 

Jagoran boko haram ya kara da cewa babu abun da jami'an tsaro zasu iya tsinana masu kuma babu abun da zasu samu daga gare su domin suna cikin inuwar Allah. Bugu da kari yana mai sanar ma jami'an  tsaro cewa babu mutumin da zai koma ga Allah sai dai idan har kwanan sa ya kare.

Har ila yau dai Shekau yana mai ikirarin cewa suna suka gabatar da hare-hare da ya faru kwanan baya a garin Maiduguri da Damboa har da Gamboru.

Har ila yau dai an rasa samun maboyar kungiyar.

A kwanan baya wani tsohon kwamandar kungiyar ya sanar cewa Shekau ya tsere dutsen Mandara domin tsira daga jami'an tsaro dake yaki da kungiyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post