Boko Haram: Buratai yayi kira ga matasan Arewa da suyi watsi da ta'adanci

Buratai urges Northern youths to shun terrorism, violence

Babban hafsan sojoji yayi wannan kiran a garin Monguna dake nan jihar Borno bayan wasan karshe na gasar cin kofin babban hafsan

Babban hafsan sojoji Tukur Bureatai yayi kira ga matasan arewa musamman wadanda ke yankin maso gabashin yankin da suyi watsi da ta'adanci, su rungumi yin aiki da zai samad da cigaba.

Buratai yayi wannan kiran a garin Monguno yayin da ake buga wasan karshe na gasar cin kofin babban hofsan sojoji tsakanin tawagar Ajeri Fc na garin Monguno da kuma River Side FC na Damasak.

Bayan wasan tamaula wanda River Fc ta samu nasara, Buratai yayi kira ga sauaran matasa da suyi amfani da karfin su wajen samun ilimi da kyakyawan basira da zai tyaimaka wajen cinma burin su a rayuwa.

Babban hafsan sojoji yayi alkawarin cewa rundunar sojoji zata cigaba da samad da damarmaki ga matasa domin nuna ire-iren basirar da Ubangiji ya basu. Yayi ikirari cewa yayin da ya ziyarci garin shekaru biyu baya garin tana fama da rashin jama'a sakamakon hare haren da yan ta'ada suka kai.

Daga karshe ya nuna godiyan sa ga Allah ganin yadda zaman lafiya ya dawo garin Moguno har ma jama'a da dama na ta dawowa garin domin cigaba ayyukan yau da kullum.

Yana mai cewa, Gasar da aka gudanar ya tabbatar cewa an samu cigaba a harkar tsaro a jihar Borno.

Post a Comment

Previous Post Next Post