Biki buduri: Tsohuwar jaruma Abida Muhammad zata sake aure

Abida Muhammed zata sake yin aure

Za'a daura aurenta da Al-mustapha Abubakar ranar juma'a 26 ga wata

Tsohuwar fitacciyar jarumar fina-finan hausa Abida Muhammed zata sake aure.

Za'a daura aurenta da Almustapha Abubakar ranar juma'a 26 ga wata a nan garin Kano dai dai karfe hudu na yamma.

*Adam Zango zai saka wando daya da masu yi masa kazafi

Jarumar zata sake aure ne bayan mutuwar tsohon mijinta Hamza Rijiyar Zaki wanda ya rasu shekarun baya.

 

Abida Muhammad tana cikin Jaruman da suka taka muhimmiyar rawa wajen farfado da masana'antar fina-finan hausa kuma tauraronta ya haska kwarai da gaske.

*Manyan jarumai sun halarci bikin taya murna zagayowar ranar haihuwar Halima Atete

 A zamanin da tsohuwar jarumar take tashe tana sahun gaba cikin jerin matan da ake ji dasu a farfajiyar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Bayan auren ta da tsohon mijin ta marigayi Hamza Rijiyar Zaki aka daina jin duriarta a dandalin fim.

Post a Comment

Previous Post Next Post