Babban kamu: Sarkin aljanu ya shiga hannun hukuma

Suleiman Umar kenan wanda yake damfarar jama'a da sunan shi "sarkin aljanu"ne

Suleiman Umar dan asalin garin Kace da ke karamar hukumar Lafai a Jihar Neja, yana zaune ne a Layin Dattawa dake Hayin Ruwa Rigasa nan jihar Kaduna.

A ranar litinin da ta gabata ce ’yan sanda suka gurfanar da wani da ake zargin ya shahara wajan damfarar jama’a da karbe abin hannunsu da sunan shi Sarkin Aljanu a gaban kotu.

Mai laifin Suleiman Umar mai shekara 37 wanda aka gabatar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare da ke kofar Fada, Zaria ana zarginsa ne da damfarar mutane ta hanyar buga masu waya yana bayyana cewa shi Sarkin Aljanu ne.

Suleiman Umar dan asalin garin Kace da ke karamar hukumar Lafai a Jihar Neja, yana zaune ne a Layin Dattawa dake Hayin Ruwa Rigasa nan jihar Kaduna.

Wani mai suna Suleiman Muhammed da ke zaune a Unguwar Liman cikin birnin Zaria, ya kai kara gaban DPO Kasim Abdul da ke ofishin ’yan sanda na kofar Fada cewa wani da ya saba damfararsa da sunan shi Sarkin Aljanu ne ya kira shi a waya cewa ya kai masa dubu N450,000 ya ajiye masa a gidin wata itaciya a Madaci da ke kan hanyar Karau-Karau.

*Saurayin da yayi ma kajin makwabcin shi fyade har suka mutu

Bayan kammala bincike ne aka tura shi kotun domin ya fuskanci shari’a, inda mai gabatar da kara Sufeta Sarki Abdullahi yace za'a tuhume shi bisa ga laifin da yake wanda ya sabawa dokokin jihar Kaduna.

Wanda ake tuhumar ya amsa wasu daga cikin laifuffukan da ake zarginsa da yi inda ya ce lallai ya sha damfarar wanda ya kai shi kara domin tsawon lokacin da suka fara hulda ya damfare shi har dubu N65,000 sai dai bai amince da cewa ya yi wa wanda yake damfarar barazana ba.

Tattaunawan shi da jaridar Aminiya mai laifin yana mai cewa: “Na koyi wannan muguwar sana’ar ce a hannun wani maigidana da ya rasu, kuma muna sana’ar ba da magungunan Musulunci ne (Islamic Medicin), to ta nan na fara, kuma na kwashe tsawon shekara biyar ina gudanar da damfara da sunan ni Sarkin Aljanu ne ta hanyar buga wa mutane waya.”

*Sanadiyar satar rago wani bawan Allah zai dukufa a kurkuku

Ya kara da cewa: “Wadansu suna amincewa tare da imani da abin da nake gaya musu wadansu kuwa har zagina suke yi. Ina shake muryata domin ina iya yin murya iri daban-daban, idan na shake muryata nakan yi muryar Sarkin Aljanu da na Galadiman Aljanu da na dan Autan Aljanu,  har da kukan awaki da na kyanwa da na jariri duk ina yi, kuma zai yi wuya ka gane. To haka nake yi idan mutum ya amince da ni sai in yi ta karbar abin hannunsa bai ganewa. Kuma a gaskiya na kwashe kusan shekara biyar ina wannan muguwar sana’a ta damfarar mutane da sunan ni Sarkin Aljanu ne, ina cewa zan ba su sa’a, ko zan yi musu kudi, ko zan bai kwa mace haihuwa, haka nake yi har in samu sa’a.  Shi kuma wannan na samu lambar wayarsa ce a wajen abokina mai suna dan Sarki. Mazaunin garin Bauchi, kuma shi Suleiman na kai tsawon shekara daya ina kiransa a waya, na fako ya turo mun katin waya na Naira dubu uku, sai kuma kudi Naira dubu 65 na karba daga gare shi, kuma wannan karon da na ce ya kawo rabin abin da ya mallaka zan gauraya in yi masa kudi ne sai asirina ya tonu.”

A wannan damfara da nake yi na samu sa’ar wani mutumin Neja inda na samu Naira dubu 200 a dunkule, sai kuma kananan kudi kamar Naira dubu 50 da sauransu, kuma a gaskiya duk cutar da na ta yi wa jama’a ba ni da komai sai fili kwata a Hayin Ruwa, Rigasa, kuma na yi nadama kuma ina rokon afuwa.” Sarkin Aljanun ya kara.

Alkalin kotun majistare Umar Bature, ya ce tunda wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa ba tare da wata gardama ba don haka a karkashin sashi na 157 na sabon kundin laifuffuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017 ya yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara 10 ko zabin biyan tarar Naira dubu 200, kamar yadda sashi na 307 na manyan laifuffuka ya kunsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post