Aminu Atiku: Dan Atiku yayi garkuwa da dan cikin shi bayan hukunci da kotu ta zantar game da rainon yara

dan dan Atiku Abubakar yaji ba dadi daga Kotu

Kotu ta baiwa tsohuwar matar shi damar cigaba da rainon yaran su Amir da Amira wanda tun ba yau suke takun saka kan batun a gaban kotu

Aminu Atiku daya daga cikin yaran tsohon matai mataimakin shugaban kasa ya saci dan cikin shi bayan kotu ta bada umarni na tsohuwar uwardakin shi ta cigaba da rainon yaran su.

Lamarin ya faru ranar laraba 10 ga wata a kotun majistare dake jihar Legas.

A bayanin da tsohuwar matar shi tayi, Aminu ya kwace yaron su Amir daga hannun ta kana ya tsere dashi bayan mai sharia Kikelomo Ayeye na kotu ta zantar da hukunci na ta cigaba da rainon yaran su.

Alkalin ta Nwabuzor-Ethel Okoh ya kara haske akan faruwar haka inda ya dora da cewa shi Aminu ya hana yaron fitowa daga cikin mota bayan ya kulle shi a ciki.

yana mai cewa "Yaron baya tare da mu. Ya kwace yaron daga hannun mahaifiyar shi, duk da hukunci da kotu ta zantar. Yanzu haka muna kokari gano inda suke.

"Tabbas ya kwace yaron kana ya ruga dashi. bamu yi tsammanin faruwar hakan, da mun sanar da mahaifiyar da ta ruga da yaran bayan hukuncin da kotu ta zantar.

Bayan kai-kawo da ake tayi kan batun wa zai samu damar cigaba da rainon yaran su, hajiya Fatima Bolori ta samu nasara kan batun.

A zaman da aka yi, kotu ta umarci Aminu da ya biya Fatima N250,000 ko wani wata domin kulawa da yaran. Hakazalika kotun ta bashi damar ziyartar yaran kuma yana iya tafiya dasu idan suna hutun makaranta.

Aminu Atiku da Fatima Bolori sunyi aure cikin 2017 amma sun rabu cikin 2011 bisa sabani da suka samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post