Aisha Alhassan tace harkar siyasa ra'ayi ne kuma babu wanda zai tilasta ta wajen barin jam'iyar da ta taimaka wajen ganin ta samu nasara
Ministan ayyuka mata Aisha Jummai Alhassan ta musanta labari dake yaduwa na cewa zata sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP inda ubangidanta Atiku Abubakar yake.
Hirar ta da jaridar Premium times ministan tace zata cigaba da zama a cikin jam'iyar APC duk da cewa a kwanan baya ta sanar cewa zata mara ma tsohon mataimakin shugaban kasa baya idan har zai tsaya takara a zaben 2019.
A bayanin ta, tana cikin manyan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen ganin APC ta samu nasara don haka bazata fice daga ita ba duk da alamu dake nuna cewa Atiku zai nemi takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'iyar adawa ta PDP.
"Siyasa ra'ayi ne kuma babu wanda ya tilasta mun wajen sauya sheka daga PDP zuwa APC a baya hakazalika babu wanda zai tilasta mun wajen barin jam'iyar. Zan cigaba da aiki karkashin APC kuma don wannan kokarin nayi tafiya zuwa jihar Taraba domin mara ma dan takarar jam'iyar Sanusi jambawaile baya.
"Na san akwai mutane da dama na son ganin na bar APC amma ina mai tabbatar masu cewa ina nan cikin jam'iyar babu ja da baya. Ta yaya zan tarwatsa ginin da muka yi kokari wajen ginawa tare?, cewar Aisha Alhassan.
Goyon bayan Atiku Abubakar
A cikin bidiyo wanda aka wallafa a intanet ranar talata 5 ga watan Satumba, ministan tare da tawagar yan jam’iyar APC na jihar Taraba suna mara ma Atiku baya wajen zama shugaban kasa.
Aisha tana cewa “ Mai girma, baban mu, shugaban kasan mu in Allah ya yarda 2019. A gaban ka mutanen ka ne magoya bayan ka har abada mutanen jihar Taraba”.
Ta kara da cewa “sun zo ban girma da gaisuwar sallah tare da yi maka murna na wannan daukakar da Allah ya kara maka, domin daukaka Allah ya riga yayi maka. Don wannan kari shine muka gan faduwa ta zo dai dai da zama, za’aje godiya shine muka ce toh dole ayi da mu”.
Bugu da kari ministan tayi karin haske game da kalaman da tayi hirar da ta BBC hausa ranar 7 ga watan satumba na bara.
*Mama Taraba ta bada hakuri game tsokacin da tayi
Ministar harkokin mata Aisha Alhassan ta bayyana cewa baza ta zabi Buhari indai ya fito takara tare da ubangidan ta Atiku Abubakar.
Bayan ganawar da tayi da jiga-jigan jam’iyar APC ranar alhamis 14 ga watan Satumba na 2017 ciki har da shugaban jam’iyar John Odigie- Oyiegun game da kalaman da ta furtar goyon bayan Atiku, babban ministan ta baiwa shugabannin jam'iyar hakuri da faruwar haka.