Ahmed Buhari: Wannan matashi yana shirin fitar da Shugaba Buhari daga fadar Aso Villa

Ahmed Buhari vows to chase President Buhari out of Aso Rock

Matashi mai shekaru 38 yace muhimmin dalilin da yasa zai fito takara shine domin ya kai kasar tudun nasira kamar yadda ya kamata.

Idan har shugaba Muhammadu Buhari na shirin zarcewa kan karagar mulki, toh lalle ya kamata ya zage damtse domin wannan matashi dan kasuwa Ahmed Buhari ya sha alwashin kawar dashi daga kujerar sa a zaben 2019.

Dan garin Kontagora dake jihar Neja kuma shugaban kamfanin Skylar Inc, Ahmed ya shaida ma jaridar Daily trus cewa ya shirya damawa a harkar siyasa kuma kujerar shugaban kasa yake nema domin ya fanshi kanshi da sauran jama'a irinshi dake korafi akan yanayin da kasar take.

 

*Idan baba ya fito takara 2019 ba zan zabe shi

Matashi mai shekaru 38 yace muhimmin dalilin da yasa zai fito takarar shugaban kasa shine domin ya kai kasar tudun nasira kamar yadda ya kamata.

Hirar shi da jaridar Business Day dan kasuwan ya sanar cewa zai fito takara ne domin ya mayar da martabar Nijeriya na zama jagoran kasashen afrika.

Bisa ga tsarin dokar kasa wannan matashin yana da yancin fitowa takara kuma da wannan yana kira ga sauran matasa da su fito takara domin kwato mulkin shugabanci daga dattijai.

 

Duk da cewa ya fidda aniyar sa na fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2019, Ahmed bai bayyana ainihin jam'iyar da zai fito domin cinma burin shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post