Ahmed Abubakar: Abubuwa  da ya kamata ka sani game da sabon shugaban hukumar NIA da Shugaban kasa ya nada

Buhari appoints Ahmed Abubakar as head of NIA

Kafin ya samu sabon matsayin, Abubakar shine babban mai yi ma shugaban kasa hidima a bangaren ayyukan kasashen waje

Ga wadansu abubuwa da ya kamata mu sani game da sabon shugaban hukumar NIA da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada.

Jiya laraba 10 ga watn janairu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin sabon shugaban hukumar hukumar tattara bayanan sirri NIA malam Ahmed Abubakar.

 

Sabon jagoran hukumar zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar Ayo Oke wanda shugaba kasa ya kora daga aiki bisa laifin wawushe kudin jama'a da ake zargin shi da yi.

Ga abubuwan game dashi kamar haka;

Kafin nadin shi shine babban hadimin shugaban kasa

Malam Ahmed Abubakar shine babban mai yi ma shugaban kasa hidima a fannin ayyukan kasashen waje.

Yayi aiki tare da majalisar dinkin duniya

Ssabon shugaban yayi aiki da majalisar dinkin duniya a bangarori da dama musaman a wajen inganta harkar sulhu da kuma bunkasa alamuran shugabanci domin inganta tsarin doka da bayar da damar tabbatar da yancin dan adam.

Yayi aikin hadimi ma dakarun soji ta musamman

Kafin ya samu matsayi na zama hadimin shugaban kasa Malam Abubakar yayi aikin mai bayar da shawara ma dajarun sojoji ta musaman na kasa da kasa wanda hedikwatar ta ke Njadmena na kasar Chadi.

Yayi karatu a jami'ar Ado Bayero dake Kano

Karatun sa na digir na farko Abubakar yayi karatu a kan harshen faransanci da adabin ta kana a karatun digir na biyu yayi ne a kan adabin harshen faransa.

Post a Comment

Previous Post Next Post