Lalle soyayya ruwan zuma ce, idan kuka kalli wannan hotunan zaku tabbatar da haka
Fitaccen jarumi kuma mai shirya fina-fina na dandali Kannywood Adam A.Zango ya kasa boye kaunar da yake dashi ga uwardakin shi.
Prince Zango kamar yadda aka fi kiran shi dashi ya sanya hotunan shi tare da matar shi Ummulkulsum a shafin shi na kafar sada zumunta ta Instagram.
Karanta>> Adam Zango zai saka wando daya da masu yi masa kazafi
Jarumin shirin "Gwaska" ya hotunan tare da kalamai soyayya wanda ke sanya zukata murmushi.
Zango ya auri Ummulkulsum wanda asali yar kasar Kamaru ce cikin shekara 2015.
Karanta>> Abubuwa 5 da ya faru a masana'antar kannywood cikin 2017
Wannan salon nuna kauna ya haifar da farin ciki ga masoyan shi inda wasu da dama suna ta mashi fatan alheri a shafin shi.
Allah ya karo dankon kauna.
Tags:
News