A jihar Kaduna: Masu garkuwa da mutane sun saki maigarin Ikulu na karamar hukumar Zangon Kataf

Cif Yohana Kukah dan uwan babban limamin cocin katolik reshin jihar Sokoto Rebren Mathew Kukah ne, kuma yana da saruta a karamar hukumar Zangon Kataf

Wadanda suka sace daya daga cikin jagororin garin Ikulu Mista Yohana Kukah, sun sake shi.

Hukumar yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da haka ranar alhamis 11 ga wata.

Kakakin hukumar na jihar ASP Mukhtar Aliyu ya sanar cewa a dai dai karfe uku na rana aka sake shi kuma babu wani alamun ciwo a tare dashi.

Gameda biya diya kakakin yana mai cewa "A kan batun fansa ta sakin shi ba zan iya tabbatar da yiuwar hakan ba."

Masu garkuwar da suka sace shi sun bukaci a biya su naira miliyan 100 kafin su sake ga iyalin shi.

"Muna iya bakin kokarin mu wajen ganin mun kama wadanda suka aikata laifin" kakakin ya kara.

Masu garkuwa da mutane sun sace Yohana Kukah wanda shine maigarin Ikulu dake karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna a daren ranar 2 ga watan farko cikin gidan shi.

Dan uwan babban faston cocin katolik reshin jihar Sokoto watau Rebren Mathew Kukah.

Post a Comment

Previous Post Next Post