A dai dai karfe 12:05 na safe maharar suka kai masa hari yayin da ake murnar shiga sabuwar shekara
Yan bindiga wadanda ake zargin cewa makiyaya ne sun harbi mai garin Numana Gambo Makama na karamar hukumar Sanga dake jihar Kaduna tare da matarsa mai dauke da juna biyu a safiyar ranar litinin 1 ga watan farko na 2018.
Mai sarautar Etum Numana ya dawo kauyen shi dake nan Arak domin taya murnar shiga sabon shekara yayin da maharar suka far masa a gidan sa dai dai karfe 12:05 na safe har suka harbe shi da matar shi da kuma dan shi.
Nan take mai garin da matar tasa suka rasu amma ya samu damar kubita har aka ruga dashi asibiti bisa raunuka da ya samu sanadiyar farmakin.
A rahoton da jaridar The Cable ta fitar, shugaban kungiyar samad da cigaba a karamar hukumar Sanga Bala Audu ya bada labarin harin.
Karanta>> Sarkin Musulmi yayi Allah wadai kan matakin da makarantar lauyoyi ta dauka kan Firdausi Amusa
Audu ya kara da cewa maharar sun calla ma gidan mai garin wuta har ma suka kona wata mota wanda aka bashi kyuatar ta kwanan baya kana suka suka ruga cikin daji.
Kakakin rundunar yan sanda na jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya tabbatar da lamarin tare da sanar cewa har lokacin da aka fitar da wannan labarin basu yi kame kame ba.