Tambuwal yayi wannan kiran ga gwamnatin tarayya ranar talata 19 ga wata yayi da yake jawabi a taron yan majalisar dattawa kan miyagun kwayoyi a jihar kano
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto yayi kira na a kawo karshen fataucin maganin mura dauke da sinadarin Codein a fadin kasar.
Tambuwal yayi wannan kiran ga gwamnatin tarayya ranar talata 19 ga wata yayi da yake jawabi a taron yan majalisar dattawa kan miyagun kwayoyi a jihar kano.
Taron wanda yan majalisa suka dauki nauyin shiraya yana daga cikin tsarin magance illar da kalubale da mayiagun kwayoyi ke haifarwa a kasar tare da neman hanyar kawar da ita.
Gwamnan wanda ya samu wakilci daga kwamishinan kiwon lafiya Dr Balarabe Kakale yace hana safarar codein ya zama dole domin kawo karshen yawan amfani da matasa keyi.
Yace yin haka ya zama tilas domin magunguna da suka kunshi sanadarin Codein ba abun ceton rayuwa bane sai dai su haifar da illa a kasa da sanya mutane maye.
A kan wannan batun ita ma wata kwararriyar likita Dr Fatima Hassan na asibitin horo ta Aminu Kano tayi kira ga gwamnatin tarayya da a haramta amfani da magungunan mura a fadin kasa.
Shima wani kwarraren mai bada magani a asibitin horo na Aminu kano, Ahmed Gana yayi kira ga gwamnatin tarayya na a kaddamar da wasu jihohi uku a matsayin masu bukatar agaji na gaggawa ganin yadda illar amfani da miyagun kwayoyi ke barazana a jihohin.
Karanta labarin>> Gwamnatin jihar Kano ta halaka miyagun kwayoyi na kimanin biliyan N4.1
Ya kara da cewa wannan zai taiamaki gwamnati wajen bude cibiyoyin kiwon lafiya masu tabin hankali domin kula da masu fama da illoli da ya danganci amfani da miyagun kwayoyi kana zai taimaka wajen mayar dasu mutane masu ki;ima a al'umma.
Daga karshe ya bukaci gwamantin tarayya da ta lura da ire-iren kwayoyi dake haifar da mummunar sakamako tare da sa ran haramta su a kasar.