Siyasa: Tsohon gwamnan jihar Taraba ya sauya sheka zuwa APC

Former Taraba Governor, Danladi, dumps PDP for APC

Wannan matakin ya faru bayan wata shidda da kotu ta tsoke shi daga kujerar majalisar dattawa

Tsohon  mukaddashin gwamnan jihar Taraba Sani Abubakr Danladi ya sanar da ficewar shi daga jam'iyar PDP zuwa APC.

A bisa rahoton da Premium Times ta fitar, Danladi ya sanar da haka mazabar shi dake nan yankin Bachama na karamar hukumar Karim Lamido ranar talata 26 ga watan Disamba.

Danladi yayi watsi da jita-jita dake yawo na cewa akwai gaba tsakanin shi da gwamnan jihar Darius Ishaku inda yake cewa "babu wata gaba tsakanin mu, shi harkar siyasa ra'ayi ne kuma nan jama'a ta ke son shiga domin kawo masu canji a wannan jihar tamu".

Game da ficewar shi daga jam'iyar, wani jigon jam'iyar PDP na jihar David Dogo yace babu wata tarzoma da ficewar shi zata haifar a jam'iyar kuma dai suna masa fatan alheri.

Karanta>> Tsohon gwamna ya bayyana Dalilin daya sa ya canja sheka zuwa jam'iyar APC

Wannan matakin da Danladi ya dauka na komawa APC yazo bayan wata shidda da kotun koli ta tsoke a matsayin dan majalisa dattawa mai wakiltar yankin arewacin jihar Taraba ta bayar da tutan ga Shuaibu Lau.

Lau dai ya kai kara kotu bisa ga rashin adalci da aka aikata bayan shine ainihin wanda ya lashe zaben jam'iyar.

Kotun ta tsayar dashi a matsayin wanda yayi nasara kuma ta tsoke Danladi daga kujerar kana ya mayar da duk albashin da alaewus da ya amsa tsakanin kwana 90 da yayi a zauren yan majalisa.

Post a Comment

Previous Post Next Post