Kan lafiyar Yusuf Buhari: Jiiga-jigan yan siyasa sun tura ma iyalin shugaban kasa Sakonnin jaje

President's son reportedly in critical condition, could be flown to Germany

Yan siyasa sunyi watsi da bambanci jam'iya da manufa domin taya shugaban kasa bakin ciki bisa ga mummanar hatsari da dan shi Yusuf ya samu

Wasu jiga-jigan yan siyasa sun jajarta wa shugaban kasa bisa ga abun bakin ciki da ya faru da dan shi sanadiyar hatsarin babur.

Yusuf Buhari ya ji rauni har da karaya sanadiyar hatsarin babur da ya samu a daren ranar 26 ga wata disamba a garin Abuja.

 

Su dai yan siyasan sun fitar da sakonin a shafukan su na kafar sada zumunta don jajantawa shugaban kasa kan lamarin.

Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda a yanzu yana kasar Liberia inda yake kula da yanda zaben kasar ya kasance ya rubuta sakon shi kamar haka

“Ina kasar Liberia inda nake kula da zabuka kawai sai na samu mummunan labarin. Iyalaina da ni kaina muna addu’a ga samun lafiyar Yusuf Buhari. Burina ne ganin matashi mai cike da kyakyawar bueri ya rayu domin ya cika burin shi. Allah yana tattare da shi."

 

Yakubu Dogara

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya rubuta "ina taya shugaban kasa da iyalen shi adua. Allah ya ba Yusuf lafiya cikin gaggawa,  Ameen.

Sanata Ben Murray Bruce

Sanata Ben Murray Bruce shima ya tofa albarkacin bakin sa ka batun inda ya rubuta  "Ina ma Yusuf fatan samun lafiya cikin gaggawa. Ina son in sanar ma Iyalen shugaban kasa cewa ni da iyali na muna tare dashi a wannan lokacin kunci kuma muna masu addu'o'i.

 

Abike Dabiri

Mai baiwa shugaban Buhari shawara ta musamman akan abubuwan da ya shafi kasar waje Abike Dabiri ta jajanta wa shugaban tare da nuna farin ciki ganin cewa Yusuf bai samu mummunar sakamako sanadiyar hatsarin.

"Muna taya shugaba Buhari da Aisha da ma iyalen su baki daya bakin cikin abun da ya faru. Alhamdulillah kasancewa Yusuf bai shiga wani mummunar yanayi ba.

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shuagaban kasa wanda ya sauya sheka daga jam'iyar APC bisa ga rashin jituwa da yanda ake gudanar da alamuran jam'iyar ya ajiye bambamci akida da jam'iya a gafe inda shima ya rubuta

"Muna taya iyalen shugaban kasa bakin ciki. ni da iyali na zamu cigaba da yi maku addu'a. Muna fatan Yusuf zai samu sauki cikin gaggawa.

Kan sakonin da iyalensa suka samu na fatan alheri da addu'o'i shugaban Buhari ya mika sakon godiya ga dinbim jama'a da suke taya shi jaje.

 

A safiyar yau dai aka tafi da shi Yusuf kasar waje inda zai cigaba da jinyar raunin da ya samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post