A kwanan baya ne dan majalisa Nnanna Igbokwe mai wakiltar jihar Imo ya sauya sheka zuwa jam'iyar APC daga jam'iyar PDP.
Tawagar yan majalisar wakilai ta jamíyar PDP sun gudanar da zanga-zanga ranar talata 19 ga watan disamba yayin da ake zaman majalisa.
Hakan ya faru ne bayan yan majalisar tawagar PDP sun nemi kakakin majalisar Yakubu Dogara ya yantar da kujerar wani abokin aikin sanadiyar wanda shi kakakin bai lamunta da yi.
A kwanan baya ne dan majalisa Nnanna Igbokwe mai wakiltar jihar Imo ya sauya sheka zuwa jam'iyar APC daga jam'iyar PDP.
Igbokwe yayi hakan ne a idon gwamnan jihar Imo watau Rochas Okorocha.
Sauya sheka da dan majalisar yayi ya haifar da tsegumi a zauren majalisar inda tawagar yan jam'iyar PDP suka nuna rashin jituwa da hakan.
Karanta labarin>> Ficewar Atiku Abubakar daga jam'iyar APC
Yan majalisar sun nuna facin ran su har suka fice daga wajen zaman majalisar.
Ficewar su daga zauren majalisar, tawagar PDP na zauren sun fice zuwa dakin taro domin tattaunawa da manema labarai kan batun.