Babban abun la'ákari shine kasancewar wuraren nan a yankin arewacin kasar ba sai kayi tafiya zuwa wani kasa ba.
Idan kana neman wuraren zuwa domin yin yawon bude ido toh lalle ka shirya ziyartar wuraren nan masu almari cike da kyawawan gurare cikin yanayin halittar Allah.
Babban abun la'ákari shine kasancewar wuraren nan a yankin arewacin kasar ba sai kayi tafiya zuwa wani kasa ba.
Ga wuraren kamar haka:
1. Mambila a jihar Taraba
Mambila Plateau kamar yanda ake kiran sa cikin harshen turanci wuri ne mai tsawo cike da wuraren alfahari daban daban.
Akwai koramu da kogo tare da tsaunuka a wannan kyakyawar wuri wanda tsawon shi ya wuce mita 1600 tsakaninsa sa da iyakar teku.
Yanayin garin kadai ya ishe kace ka shiga kasar waje.
2. Koramar Matsirga a Kafanchan nan jihar Kaduna
A kauyen Madakiya dake karamar hukumar Kafanchan nan jihar Kaduna zaá samu wanan koramar wanda tsawon shiya kai mita 30.
3. Ganuwar Kajuru a Kaduna
Ganuwar Kajuru kebatacciyar wuri ne kuma wurin hutawa na kasaita wanda aka gina tun zamanin da. Yana nan garin Kajuru dake nan jihar Kaduna.
Abun lura da game da wurin shine yanayi kerar ginin tare da kyawawan yanayin haraba dake cikin ta idan bako na kallo daga masaukin sa.
4. Gurara na jihar Neja
Nan jihar Neja za'a sami wannan korama wanda wani mafarauci mai suna Buba ya gano cikin shekara 1745.
5. Tsaunin shere a garin Jos
Tsaunin shere yana cikin manyan wuraren zuwa na yawon bude ido a arewacin Nijeriya.
6. Gandun daji a Yankari
Shine wuren zuwa yawon bude ido mafi farin jini kana shine mafi girma a fadin Nijeriya.
Ga mai sha'war ganin dabbobin daji da kyawawan bishiyoyi da fure na alfarma tare da yin waka cikin korama mai fitar da ruwan dimi, sai ya garzaya garin Yankari dake nan jihar Bauchi.