Amiu Masari: Ficewar Atiku daga APC bata haifar da koma baya

Aminu Masari

Yace sauya shekan da tsohon mataimakin shugaban kasa yayi zuwa jam'iyar adawa ta PDP baza ta hana jam'iyar APC samun tasiri a zaben nan gaba.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yayi tsokaci game da ficewar Atiku Abubakar daga jamíyar APC inda yake cewa babu wata fargaba da ficewan shi zata kawo ga jam'iyar.

Yace sauya shekan da tsohon mataimakin shugaban kasa yayi zuwa jam'iyar adawa ta PDP baza ta hana jam'iyar APC samun tasiri a zaben nan gaba.

 

Yayi wannan maganar ne ranar litinin a karamar hukumar Maiadua yayin da yake ganawa da manema labarai a taron tarban tsohon kakakin majalisar jihar Katsina watau Alhaji Yau Gwajo Gwajo wanda ya sauya sheka zuwa APC daga jam'iyar PDP.

Karanta labarin>> Shugaba Buhari yayi dana sani, ficewar Atiku daga jam'iyar APC

Gwamnan yace zamanin siyasa ta hanyar kama karya ya wuce domin a yanzu halin mutum da ire-iren ayyukan alkhairi da yayi ke taimaka masa a fagen siyasa.

Masari yace a shirye jam'iyar APC take wajen karban sauran jama'a dake da niyyar dawowa ko sauya sheka zuwa jam'iyar domin yana mai kyautata zaton cewa nan ba da jimawa ba za'a samu dinbim mutane a karkashen jam'iyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post